Bayanai sun ce 'yan Boko Haram din sun kaddamar da harin ne a lokacin da ake cin kasuwar garin.
Kawo yanzu babu bayanai game da adadin wadanda suka rasu, amma wasu majiyoyi sun ce kananan yara da 'yan kasuwa na daga cikin wadanda aka hallaka.
Bayanai sun ce an kai gawarwakin wasu daga cikin wadanda aka kashe zuwa asibitin gwamnati na birnin Maiduguri.288